Steve Lucas ya fara aiki da Muryar Amurka a matsayin mai labaran Hausa. Daga nan ya zamo shugaban Sashen Hausa, ya kuma zamo shugaban Sashen Afirka baki daya. Steve Lucas ya kuma rike mukamin darektan ofishin hulda da gidajen rediyon Afirka. Kuma kafin ritayarsa, shi ne darektan ofishin hulda da gidajen rediyon duniya na Muryar Amurka.
Sashen Hausa ya yi hira da mutane kalilan da suka yi aiki da marigayi Steve Lucas da suka hada da wakilai na da, da na yanzu, da wadanda ya koyawa aikin jarida da kuma wasu shugabanni a Muryar Amurka wadanda suka suka bayyana shi a matsayin mai son mutane da mutunta abokan aiki da kuma darajanta iyali.
Mohamed Abdelkader ya dade yana sauraron Sashen Hausa ya kuma shaku da Steve Lucas. Ya bayyana cewa, ya fara sauraron Muryar Amurka tun yana karami kuma abinda ya kara daukar hankalinshi da ya sa ya nace sauraron Muryar Amurka shine jin Bature yana Hausa tsantsa.
A nashi bayanin, Idy Bara’u, tsoho wakilin BBC kuma babban aminin Steve Lucas, ya bayyana irin dangantaka ta kut da kut da ke tsakainsa da marigayi Steve, da bisa ga cewarshi suka fara tun yana matashin dan jarida, a lokacin Steve yana babban darekta a Muryar Amurka. Ya bayyana cewa, Steve ya burge shi ganin yadda yake mu'amala da bakakken fata ya ci kowanne irin abinci ba kyama.
Ya kuma bayyana irin baiwar da Allah ya yi wa Steve a harshen Hausa da kuma sha'awar da Steve ya nuna ta renon 'yan jarida masu tasowa.
Shugaban Sashen Hausa, Aliyu Mustapha na daya daga cikin wadanda suka yi aiki da Steve Lucas na lokaci mai tsawo wanda banda kasancewa shugabansa a wurin aiki, ya kuma zauna a gidan Steve na dan lokaci inda ya ce Steve ya rika dafa masu tuwo miyar kuka da daddawa kamar yadda aka saba gani a gidan Hausawa.
A nashi bayanin, tsohon darektan Sashen Afrika Negussie Mengesha da ya yi ritaya kwanannan, ya bayyana Steve Lucas a matsayin mutumin kirki wanda ya ce shine ya daga matsayinshi a Muryar Amurka daga shugaban Sashen Afrika ta tsakiya ya maida shi mataimakinsa, lokacin Steve yana darektan Sashen Afrika. Abinda ya ba shi Negussie damar zama shugaban Sashen Afrikan bakin fata da ya fito daga wata kasar Afrika na farko.
Ya kuma bayyana irin kyakkyawar dangantakar aiki da ya yi karkashin marigayi Steve Lucas.
A lokacin da Steve Lucas ya yi ritaya daga Muryar Amurka a shekara ta dubu biyu da takwas, ya ce babban dalilin da ya sa yanke shawarar komawa Nijar ya zauna da iyalinsa da zarar ya yi ritaya shine domin 'yarshi Zainab wadda a lokacin tana da shekaru uku da haihuwa ta sami tarbiya.
Steve ya bayyana cewa, ba ya jin dadin ganin yadda ake barin yara suna tashi kara zube a Amurka babu tarbiya, da kuma yadda yake ganin rayuwar matasa tana kasancewa. Yace ba ya so 'yarshi ta girma cikin wannan yanayin ko ta tashi da irin wannan rashn tarbiyar, dalili ke nan da ya sa ya zabi komawa NIjar da zama inda za ta girma cikin al'adun da ya tashi, domin bisa ga cewarshi hakan zai fi zama da alheri da kuma amfani a gare ta.
A hirar ta da Sashen Hausa kwana daya bayan rasuwar Steve, mai dakinsa Fatouma ta bayyana shi a matsayin babban abokinta wanda ya ke kaunar Afrika da kuma Amurka. Bisa a cewarta, Steve mutum ne mai son mutane da kuma mutunta kowa, wanda ya rungumi ba danginta na kurkusa kadai ba, amma dukan al'ummar Jamhuriyar NIjar da kuma sauran kasashen Afrika da yayi aiki.
Daga cikin wadanda aka sa hirarrakin su a wannan shirin akwai Marigayi Sani Abdullahi Tsafe wakilin Sashen Hausa na farko wanda ya fi kowanne wakili sanin Steve Lucas wanda aka yi hira da shi a lokacin da Steve ya yi ritaya..
a-39-2008-08-01-voa1-91724104/1369301.html
Saurari cikakken shirin domin jin wadannan hirarraki masu ban sha'awa da sosa rai:
Your browser doesn’t support HTML5