A BARI YA HUCE: Labarin Sarakan Karya, Satumba, 26, 2020

Alheri Grace Abdu

Wasu abokai ne suna zaune suna hira sai dayan ya cewa abokinsa , kai duniya ana abubuwan mamaki sai abokin yace, menene kuma ya faru ? Sai abokin yace, shekaran jiya ne ina zaune kusa da wata kwata, sai ga wata mata mai ciki tazo zata tsallaka. Sai naji dan cikin nata na cewa, " Ina kwana Baba?" Sai Matar da ta ji haka ta dube ni tace mun, "kana kama da Babansa shi yasa ya gaida kai". Sai abokin nasa ya ja tsaki yace, to wannan ma har wani abun mamaki ne? Ni da aka yima abinda na kusa suma a tsaye. Abokin ya tambaye shi, menene aka yi maka?. Sai abokin yace mun shiga mota ne daga Kaduna zamu je Kano. Ashe ba mu sani ba tun fitar mun Kaduna direban motar mu ya rasu, amma bamu sani ba, sai da muka zo Kano. Munje gidan mai, motar ta tsaya za a sha mai, aka tambayeshi na nawa za'a zuba? aka ji shuru, da mai sayar da mai ya je gefensa sai aka ga ashe direban ya rasu, har ma ya sandare. Da abokin ya ji haka haushi ya kama shi, ya ce wallahi tallahi, karya ka ke.

Saurari cikakken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

A BARI YA HUCE: Labarin Sarakan karya-28:00"