Wani Babarbare ne ya je kasuwa ya sayi tangaran da yawa, da ya daga ya ji nauyi ya rasa yadda zai yi ya kai shi gida shi kuma ba shi da kudin dako, sai ya hango wani Bafullatani can yana tsaye yana hira, ya kira shi, ya ce mashi, Jauro, ka daukar min kayan nan nawa ka kai min gida, ni kuma zan gaya maka wasu abubuwa guda uku da za su amfane ka har iya rayuwarka, Da jin haka sai Bafillatani ya ce ya amince. Ya dauki buhu da kyar yana nishi ya dora a baya , suka yi ta tafiya.
Da suka yi nisa sai Bafullatani ya ce wa Babarbare, ka fada min abubuwan uku. Babarbare ya ce abu na daya shine, duk wanda ya ce maka da koshi gara yunwa kar ka gaskata shi. Bayan sun ci gaba da tafiya sai Bafullatani ya ce to na biyu fa? Sai Babarbare ya ce, na biyu, duk wanda ya ce maka da tafiya kan abin hawa gara tafiya a kasa karka gaskata shi.
Saurari cikakken shirin ka ji abu na uku, ka kuma gaya mana wanda aka fi cuta.
Facebook Forum