A Bari Ya Huce: Labarin Barawon Masara Da Masu Gona-Satumba, 05, 2020

Alheri Grace Abdu

Wani manomi ne ya shuka masara a gonarsa, da masarar ta nuna sai ya lura kullum ya je gonar sai ya tarar an saci masara, ya rasa wanda yake shiga gonar. Wannan lamarin ya dame shi ya rasa yadda zai yi, sai wata rana ya ce dansa ya je ya wuni a gonar ya yi gadi. Dan bai jima da isa gonar ba sai barawon masara ya shiga ya hau karya yana turawa buhu, shi kuwa yaron yana wani wuri ya labe yana kallo. Da ya lura hankalin barawo ya koma kan karyar masara sai ya yi sando ya cukume barawon, ya kuma yi sa'a ya fi barawon karfi ya yi ta janshi zai kai shi wurin mahaifinsa.

Da barawo ya ga sun kusa shiga gari ya kuma san ba za a kwashe da mara ba idan har aka kai shi gaban mai gona, sai ya yi dabara ya tsaya ya cewa yaron "af ai na manta takalmina a cikin gonar, bari in je in dauko" , sai yaron a cikin fushi ya ce wa barawon, kaji shashasha: "to yi sauri ka dauko ka dawo ina jiranka a nan" ya saki barawo, shiru-shiru har rana ta fadi barawo bai dawo ba, sai yabi sawu har zuwa gona ba barawo ba alamarsa.

Da dawowarsa gida ya shaidawa babanshi ai ya yi sa'a ya kama barawon, baban ya shiga murna ya tambayeshi to ina yake, sai yaron ya fadi mashi abinda ya faru. Da jin haka uban ya fusata ya kaurawa yaron mari ya ce da shi "menene yasa ba zaka ce shi ya zauna ya jira ba kai kaje ka dauko masa takalmin?"

TAMABAYA: Wanene ya fi wauta tsakanin uban da dansa?

sausari cikakken shirin

Your browser doesn’t support HTML5

A Bari Ya Huce: Labarin Barawon Masara Da Masu Gona-28:00"