WASHINGTON, DC —
A wannan shirin, Ali Na Mailaya wani ba'are a Jamhuriyar Nijar ya maida martani bisa labarin da aka bada makon jiya.
Na Ali ya bada labarin wata Bafullatana da mijinta ya sayo mata tsarabar madubi, da yake wannan ne karon farko da ta duba madubi,da ta ga kanta a ciki ta zaci mijinta ne ya yi mata kishiya sai ta yi yaji ta tafi da madubin gida da nufin nunawa iyayenta amaryar da take tunanin mijinta zai auro. Ko da ta mikawa mahaifiyarta madubin ita ma ta ga kanta a ciki sai ta ce, " ca nike ma wata kyakkyawar budurwa ya samo da ta fi ki kyau yake so ya aura, ashe tsohuwa ce" ba ta san cewa kanta take kallo a madubin ba.
Saurari cikakken shirin:
Facebook Forum