A BARI YA HUCE: Karrama Marigayi Ibrahim Abdul'aziz, Fabrairu 06, 2021

Ibrahim Abdul'aziz

Ibrahim Abdul'ziz wanda kafin rasuwarsa ya ke dauko wa Sashen Hausa rahotanni daga jihohin Adamawa da Taraba, ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyar shi zuwa Bauchi domin halartar daurin auren abokinsa.

Abdul'aziz yana daya daga cikin hazikan wakilan Sashen Hausa wanda banda rahotanni da yake daukowa, loto-loto ya kan jagoranci gabatar da shirye shirye na musamman a Sashen Hausa. Ya kuma nuna kwarewa wajen dauko rahotannin da suka shafi rayuwar talaka ta yau da kullum, da zamantakewar al'umma ,da kuma harkokin siyasa.

Saurari wannan shirin na musamman da aka shirya domin karrama marigayin:

Your browser doesn’t support HTML5

A BARI YA HUCE: Tunawa da rayuwar Ibrahim Abdul'aziz-24:00"