Wata kiddidigar da Hukumar Aikata Manyan Laifukka ta FBI, bayyana ta nuna cewa ‘yan sanda 86 aka kashe yayin da suke bisa kan aiki a Amurka a cikin shekarar da ta gabata ta 2015.
Kamar rabin duk wadanan mace-macen duk sun faru ne a bisa hatsurra amma 41 daga cikinsu ta hanyar kisan kai ne.
Sannan kuma daga cikin ‘yan sanda 41 da aka kashe, 8 an hallaka su ne lokacin da suka je bincikar rahottanin da aka bayar na cewa wasu abubuwan da ba’a amincewa ba suna faruwa, 7 kuma an kashe su ne lokacin da suka ja daga da wadanda suka je tinkara, yayin da ‘yansanda 6 kuma sun rasa rayukkansu ne lokacin da suka tsaida wasu masu anfani da abubuwan hawa akan tituna.
Haka kuma a cikin shekarar da ta gabata, ‘yan sandan Amurka sama da dubu 50 aka kai hari a kansu, amma 30% nasu kawai suka sami raunukka.