Hukumar dake kula da al’amuran yanayi ta kasa a Amurka, ta yi gargadin cewa za a sake fuskantar gobarar daji mafi muni a kudancin California, tare da ayyana karancin danshi da sake bayyanar iska mai karfi.
WASHINGTON DC —
Ofishin hukumar hasashen yanayi na Los Angeles NWS ya wallafa a dandalin X cewa “Ku dau matakan kariya a gidajen ku da iyalan ku domin daga gobe za a fuskanci wata sabuwar matsanaciyar iska da yanayin gobara: za a fuskanci iska mafi muni a ranar Litinin da rana zuwa safiyar Talata”
Karen Bass magajiyar garin Los Angeles, ta ce, “Akwai bukatar kowa ya kasance cikin shiri.”
Akalla mutane 27 ne suka mutu a gobarar dajin farko da ta karade Los Angeles, yayin da ma’aikatan kwana kwana suke ta kokarin shawo kan wutar. Ana kyautata zaton adadin wadanda suka mutu zai karu.