An Tanadi Matakan Tsaro A Washington Don Bukin Rantsar Da ShugabaTrump

A supporter of US President-elect Donald Trump walks past a security barricade near the US Capitol in Washington, DC, on January 19, 2025, one day ahead of Trump's inauguration. (Photo by ANDREW CABALLERO-REYNOLDS / AFP)

Hasashen fuskantar matsanancin sanyi a wunin yau Litinin ya sa Trump ya sa aka mai da bukin rantsarwar cikin majalisar dokokin Amurka sannan aka mai da faratin ban girman da aka saba yi a bukin rantsarwar Capital one Arena.

Har yanzu ba a cire shingayen karfe da kankare da shingyen jami’an tsaro da aka Sanya akan tituna inda mutane ke bi a kafa a titunan National Mall ba wanda ya ratsa har majalisar dokokin Amurka har zuwa wasu mahimman wurare a Washington, yayin da ake Shirin rantsar da shugaban kasar na 47.

Sai dai, filin da girman sa ya kai kwatankwacin kadadada 146, wato kilomita 0.6 wanda galibi mutane suke kai Ziyara yanzu, bashi ne aka mai da hankali akai ba don tabbatar da tsaro.

Hasashen fuskantar matsanancin sanyi a wunin yau Litinin ya sa Trump ya sa aka mai da bukin rantsarwar cikin majalisar dokokin Amurka sannan aka mai da faratin ban girman da aka saba yi a bukin rantsarwar Capital one Arena.

Metal Barricades in place on C, Street Washington DC in preparation for President Trump Inauguration.

Canje canjen da aka sanar a ranar jumma’a sun gabatar da kalubale ga jami’an tsaro da masu tabbatar doka da oda wadanda suka dade suna shirye shiryen bukin rantsarwar tun daga bara.

Sannan ya Sanya su da kimanin jami’an tsaro da sojoji dubu 25,000 da mabanbantan kalubaloli.

Kamfanin dillancin labari na AP ya ruwaito cewa, yayin wata ganawa da manema labarai, Matt McCool na hukumar leken asirin Amurka y ace “Za mu kwashe kayakin nan.”

“Ba mu rage yawan kayakin da muka tanadar tun fark oba,”. “Ina da kwarin gwiwar cewa tare da wadanda muke hadaka da su a nan, zamu kasance cikin shiri.” Ya yiwu, alkaluman zasuyi tasiri akan

Wadanda suka shirya taron suna kyautata zaton baki 250,000 ne aka akikewa takardun gayyata da zasu ziyarci majalisar dokokin da National Mall don kalon bukin rantsarwar.