Babu Batun Karin Farashin Litar Man Fetur A Najeriya- IPMAN

Kungiyar dillalan Man Fetur ta IPMAN, ta musanta jita-jitar da ake yadawa na karin farashin litar man fetur a Najeriya.

Kungiyar ta ce, yanzu matatun man kasar na aiki, kuma hakan zai sa farashin litar man fetur ya ci gaba da saukowa. Sai dai manazarta na ganin babu wani sauki da za a samu a farashin litar man fetur a kasar.

Bayan farin ciki da ‘yan Najeriya ke yi na saukar farashin litar man fetur a makonnin da suka gabata, sai gashi yanzu murna na son komawa ciki, ganin yadda manyan dilalan man fetur masu manyan rumbun adana mai ko kuma depot, suka kara farashin litar man fetur da na gas a kasar.

A hirarsa da Muryar Amurka, Bashir Salisu Tahir dake matsayin shugaban kungiyar dilalan man fetur ta IPMAN Reshen Arewa Maso Yammacin Najeriya, ya musanta wannan zargi na karin farashin litar man fetur, ya kuma shaida cewa babu wani mamban kungiyar su da ya kara farashin litar man fetur a kasar.

Tahir, ya ce “yanzu kasuwa ce ke samarwa kanta farashi, kuma batun karin farashin litar man fetur a kasar babu shi”.

Shugaban na IPMAN ya kara da cewa “duk da cewa an samu karin farashin man dizel a ‘yan kwanakin nan, farashin sa ne ya tashi a kasuwa, kuma idan farashinsa ya sauko, to tilas za a sayar da shi a farashi me sauki”.

Tahir, ya kara da cewa “yanzu matatun man kasar sun fara aiki, don haka farashin man fetur zai sauko.”

Imarana Wada Nas, shugaban kungiyar rundunar talakawan Najeriya, ya ce babu wani farin ciki da ‘yan kasar ke yi game da yadda ake samun sassaucin farashin litar man fetur a kasar, idan aka kwatanta da yadda farashin sa yake a shekarun baya.

Imarana, ya kara da cewa “idan aka yi la’akari da yadda farashin kayan cimaka da na wutar lantarki suka tashi a kasar, babu wani abin murna a yanzu”.

‘Yan Najeriya dai na ci gaba da hankoron ganin matakan da Gwamnatin kasar zata samar da zai kawo musu saukin rayuwar da janye tallafin man fetur ya jefa su a ciki.

Saurari rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Babu Batun Karin Farashin Litar Man Fetur - IPMAN