Hukumar Hasashen yanayi ta kasa ta ce, ana kyautata zaton za a samu iska mai karfin maki Kph 80 da guguwa mai karfin Kph 110, wanda ka iya haifar da babbar damuwa ga mazauna yankunan Los Angeles. Masu hasashen sun bayyana iskar da "Yanayi mai hadarin Gaske".
Daga cikin manyan gobara uku da har yanzu ke ci gaba da ci a yankin Los Angeles, ma'aikatar gandun daji da dakile gobara ta California, ta ce an shawo kan kashi 14 cikin 100 na Gobarar Palisades, sannan kuma ta lakume murabba'in kilomita 96.
Iska mai karfi da busasshen yanayi a yankin da ba a samu ruwan sama ba sama da watanni takwas, ya taimaka wajen rura wutar gobarar da ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 24 tare da yin barna ta biliyoyin daloli.
Gobara ta lakume gidajen attajirai da fitattun mutane da talakawa baki daya, tare da mayar da wurin kamar an yi yaki. Jami'ai sun ce akalla gine-gine 12,300 suka lalace ko kone kurmus.
Gwamnan California Gavin Newsom ya bayyana gobarar da mafi munin bala'i a tarihin Amurka, wadda ta lalata dubban gidaje tare da tilasta wa mutane 100,000 tserewa.