Wata Tawaga Karkashin ECOWAS Ta Raba Kayan Tallafi Ga Al’ummar Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Bauchi

ECOWAS

Tawagar mai karfi daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta raba kayan tallafi ga al’ummar da ambaliyar Ruwan sama ta yi wa barna a jihar Bauchi a shekarar bara.

A wannan tawaga da ke karkashin Kungiyar ta ECOWAS akwai ma’aikatar kasashen ketare da ma’aikatar kulawa da agaji da rage radadin talauci ta tarayya da hukumar agaji ta Red Cross. An kiyasta tallafin kudin kan dalar Amurka Dubu Dari Biyu ($200,000).

A cikin watan Disamban bara Kungiyar ta ECOWAS, karkashin shirinta na gaggawa ta taimaka wa magidanta dari takwas da hamsin (850) a Kananan hukumomin Katagun, Jama’are, Zaki, Gamawa da kuma Giade, ana kyautata zaton magidanta guda dubu daya sun amfana da shirin bada agajin.

A jawabinta a madadin kungiyar ECOWAS daraktar agajin gaggawa Dr. Sintiki Tarfa Egbe ta yaba wa gwamnatin jihar Bauchi sabili da irin rawar da take takawa wajen kyautata rayuwar mutanen da iftila ya shafa.

Kwamishinar ma’aikatar jinkai ta jihar Bauchi Hajara Yakubu Wanka ta bayyana irin tallafin da jihar ta samar wa mutanen da ambaliyar ta yi wa barna a daminar bara.

Sashen bada agaji na Kungiyar Bunkasa tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ya fara ayyukan a Najeriya ne a shekarar dubu da ashirin da biyu, kuma a halin yanzu akalla jiha guda ta amfana daga shirin daga shiyyoyi shida na kasar Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad:

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Tawaga Karkashin ECOWAS Ta Raba Kayan Tallafi Ga Al’ummar Da Ambaliyar Ruwan Ta Shafa A Bauchi