Wani direba ya afka da motar akori kura cikin dandazon jama'ar da ke bikin shigowar sabuwar shekara a garin New Orleans na na jahar Louisina ta Amurka, sannan ya kuma bude wuta, inda ya kashe mutane 15 tare da jikkata wasu fiye da 35.
hukumar FBI mai yaki da manyan laifuffuka a Amurka ta ce, tana gudanar da bincike kan harin da ta kira a matsayin harin ta'addanci, kuma ta yi imani cewa direban ba shi kadai ya yi aika-aikar ba.
Alethea Duncan, mataimakiyar wakili ta musamman mai kula da ofishin FBI a New Orleans, a wani taron manema labarai ta ce, Ofishin yana binciken daruruwan mutanen da ake zargi.
Kamfanin dillacin labarai na Associated Press ya bayar da rahoton sanarwar hukumar leken asirin 'yan sandan jihar Louisiana cewar, Masu bincike sun gano na'urori masu fashewa da yawa a unguwar French Quarter, Sanarwar ta ce daga cikin na'urorin har da wasu bama-bamai guda biyu da aka boye a cikin na'urorin sanyi kuma an yi su ne yadda za’a iya tayar da su daga nesa.