Rasha Tace Jirgin Saman Azerbaijan Ya Yi Kokarin Sauka Ne Yayin Harin Jirgin Maras Matukin Da Ukraine Ta Kai
A yau Juma’a, shugaban hukumar kula da sufurin jiragen saman Rasha yace jirgin saman Azerbaijan da ya fadi a Kazakhstan ya yi kokarin sauka a birnin Grozny na yankin Chechen a yayin da jiragen Ukraine marasa matuka ke kai masa farmaki.
Jirgin mallakin kamfanin jiragen saman Azerbaijan ya rikito kusa da birnin Aktau na Kazakhstan a larabar da ta gabata bayan da ya yi kokarin sauka a Grozny daga nan sai ya baude zuwa wuri mai nesa a tsallaken tekun Caspian.
38 daga cikin mutanen dake cikin jirgin sun mutu, inda wasu rahotanni ke hasashen yiyuwar na’urorin tsaron sararin samaniyar Rasha ne suka harbo shi a bisa kuskure.
Wani fasinja da ya tsallake rijiya da baya ya shaidawa tashar talabijin ta Rasha cewa yaji kamar karar wata fashewa daga wajen jirgin kafin daga bisani baraguzan abubuwa masu fashewa suka fantsamo cikin sa