washington dc —
A yau Litinin, majalisar zartarwa ta tarayyar Najeriya ta amince da sauya wa jami'ar Abuja suna zuwa ta Yakubu Gowon.
Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma, Muhammad Idris ne ya bayyana wa manema labaran fadar shugaban kasa hakan a Abuja biyo bayan taron majalisar na karshe a 2024 da ya gudana a fadar Aso Villa, da ke Abuja.
An kafa jami'ar Abuja da ake yiwa lakabi da "UNIBUJA" a shekarar 1988 da nufin gudanar da tsarin karatu na gama-gari da na yin karatu daga nesa.
Jami'ar ta fara gudanar da karatu a 1990 da bikin daukar dalibanta na farko.
Yakubu Gowon tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya ne wanda ya jagoranci kasar daga 1966 zuwa 1975.