Ofishin Jakadancin Amurka Ya Fitar Da Sabon Umarni Ga ‘Yan Najeriya Masu Neman Biza  

A cewar bayanan dake shafin yanar gizon ofishin jakadancin, ziyarar farko za ta kunshi “nazarin takardun da mutum ya gabatar” tare da jami’in karamin ofishin jakadancin. Ziyarar ta 2 za ta kasance ganawar neman bizar da kanta,

Ofishin Jakancin Amurka a Najeriya ya sanarda sabunta tsarinsa na neman iznin shiga kasar ga masu son yin kaura, da zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2025.

Za a bukaci masu neman bizar da aka tsara ganawa da su su ziyarci karamin Ofishin Jakadancin Amurka dake Legas a matsayin wani bangare na sabon tsarin.

Ofishin jakadancin ya wallafa a shafinsa na X cewa “ga masu neman bizar da aka shirya ganawa da su bayan ranar 1 ga watan Janairu mai kamawa, za a bukacesu su ziyarci karamin ofishin jakadancin Amurka dake Legas akalla sau 2 a yayin da suke neman iznin shiga kasar domin yin kaura.

A cewar bayanan dake shafin yanar gizon ofishin jakadancin, ziyarar farko za ta kunshi “nazarin takardun da mutum ya gabatar” tare da jami’in karamin ofishin jakadancin.

Ziyarar ta 2 za ta kasance ganawar neman bizar da kanta, da wani jami’in ofishin jakadancin zai gudanar. Kuma cibiyar neman biza ta Amurka (NVC) ce za ta shirya ganawar.

Manufar wadannan sauye-sauye a cewar ofishin jakadancin shi ne, inganta ayyuka tare da rage jinkirin da shigar da bayanai rabi da rabi ke janyowa.

Kamar yadda aka sanar tunda fari, a wani al’amari mai nasaba da wannan, ofishin jakadancin ya sauya kamfanin dake gudanar da ayyukansa na sama da biza ga ofisoshin jakadancinsa da ke Abuja da Legas a ranar 26 ga watan Agustan, 2024.