'Yan Ghana Na Zaben Shugaban Kasa

Zaben Ghana

Za a shafe kwanaki kafin sanin sakamakon zaben.

Masu zabe a Ghana zasu yanke hukunci a yau bayan wani zabe mai cike da sammatsi da ka iya mayar da John Dramani fadar shugaban kasar Ghana ko kuma ya baiwa Dakta Mahmudu Bawumia damar zama shugaban kasar yammacin Afirka.

Abokan hamayyar sun shafe ranakun karshe na yakin neman zabensu suna kokarin yiwa magoya bayansu kaimi domin su fito suyi zabe tare da kokarin shawo kan duk mai niyar zaben da bai yanke dan takarar da zai zaba ba ya zabe su.

An bude rumfunan zabe da misalin karfe 7 na safe kuma ana sa ran miliyoyin masu zabe su kada kuri’unsu.

Za a shafe kwanaki kafin sanin sakamakon zaben.