Daruruwan Mutane A Chadi Sun Bukaci Dakarun Faransa Su Fice Daga Kasar

CHAD-FRANCE-DEMO

Kimanin mutane 500 dauke da kwalaye dauke da sakon cewa “a haramta Faransa” ne suka yi dafifi a filin wasa na N’djari Lullube da launukan tutar kasar,

Daruruwan jama’a ne suka gudanar da gangami a birnin N’djamena a yau Juma’a domin nuna goyon baya ga sanarwar da gwamnatin Chadi ta fitar a makon da ya gabata ta yanke duk wata alakar soji da tsohuwar kasar da ta yi mata mulkin mallaka, Faransa.

Kimanin mutane 500 dauke da kwalaye dauke da sakon cewa “a haramta Faransa” ne suka yi dafifi a filin wasa na N’djari Lullube da launukan tutar kasar, kamar yadda wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana.

CHAD-FRANCE-DEMO

“Bayan shafe shekaru 60 muna hadin gwiwa, bama bukatar dakarun sojin Faransa, muna da namu sojan, zamu iya kare kasarmu,” kamar yadda babban sakataren majalisar kolin harkokin addinin Musuluncin kasar, Abdel Daim Abdallah Ousmane, ya shaidawa AFP yayin gangamin.

“Zanga-zangarmu ta lumana ce. Mu ba abokan gabar Faransa bane kuma Faransa ba ta gaba da Chadi,” ya kara da cewar.

CHAD-FRANCE-DEMO

Hukumomin kasar sun amince a gudanar da zanga-zangar.

An haramta gudanar da gangami a babban birnin Chadi, duk da cewa hukumomin kasar basu hana kananan kungiyoyi yin tarurruka ba.

CHAD-FRANCE-DEMO

Faransa nada kimanin dakaru 1, 000 a tungar sojinta na karshe a yankin sahel.

Ku Duba Wannan Ma Chadi Ta Yanke Huldar Tsaro Da Faransa, Rasha Na Samun Karbuwa A Yankin Sahel

Sai dai a ranar 28 ga watan Nuwamban da ya gabata Chadi ta sanar da aniyarta ta kawo karshen kawancen tsaro tsakaninta da birnin Paris tun bayan samun ‘yancin kanta a 1960.