Rabon Tallafi Ya Janyo Kace Nace Tsakanin Tarayyar Turai da Gwamnatin Nijar

A Nijar an gabatar da bukin bayar da tallafin kudaden kungiyar Tarayyar Turai ga wasu kungiyoyi

Tarayyar turai ta janye jakadanta daga jamhuriyar Nijar domin ta ji ta bakinsa bayan da gwamnatin rikon kwaryar kasar ta zarge shi da saba ka'ida da saka son rai wajen kasafta wani tallafin kudi na euro milion 1.3 da kungiyar ta bayar domin taimaka wa 'yan kasar ta Nijar wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

Wannan ya sa ‘yan kasar suke bayyana ra’ayoyi mabambanta kan wannan kace nacen.

Wakilin Muryar Amurka a birnin Niamey a jamhuriyar ta Nijar Souley Moumouni Barma ya ruwaito cewa wannan dabarwar tada ta kunno kai tsakanin hukumomin Nijar da tarayyar Turai ta biyo bayan da sanarwar da ma'aikatar harakokin wajen Nijar ta fitar cewa akwai alamun rashin haske tattare da wani tallafin kudade euro milion 1.3 da kungiyar ta bayar don taimaka ma mutanen da ambaliyar daminar bana ta yi wa barna.

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ICRC da kungiyar kula da 'yan gudun hijra Danish refugee council DRC da Cooperazione internationale COOPI sune kungiyar ta EU ta bai wa wadannan kudade, abinda hukumomin Nijar suka ce an yi shi cikin yanayin mai hazo. Hasali ma, jakadan kungiyar da kansa ne ya karkasa wannan tallafi a tsakanin jihohi duk ko da cewa a ka’ida a kan yi irin wannan aiki ne da hadin guiwar gwamnati.

A bayanin da yayi kan wannan al’amari, shugaban gamayyar kungiyoyin Reseau Esperance Bachar Mahaman ya ce, Tarayyar Turai ba ta yi la’akari da sabuwar tafiyar Nijar ta yau ba a yayin bayar da wannan tallafin.

Da take maida martani kungiyar EU ta bayyana takaici akan abubuwan da ta ayyana da zarge zarge marassa tushe sannan ta kara da cewa bai dace a siyasantar da aiyukan Jin Kai ba.

A sanarwar da ta fitar, kungiyar tace a kullum ta na shirye don baiwa al’ummar Nijar taimako.

A latsa nan domin sauraron rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

(1) - 11_24_24 EU RECALL ITS AMBASSADOR FROM NIGER.wav