Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Shehu Mohammad Dalijan wanda ya gabatar da wadanda ake zargi da aikata laifuffaka daban daban su 22 a hedikwatar ‘yan sanda, da ke Gusau a yau Talata ya ce wadanda ake zargin sun hada da wani mai kera bindigogi kirar AK 47 da kuma bindigogi kirar SMG wanda aka kamo daga jihar Filato.
Kwamishinan 'yan sandan ya ce rundunar ta kuma kama wasu da ake zargi da suka hada da masu samar da kayan aiki ga ‘yan bindiga wadanda aka kama su da tsabar kudi Naira miliyan biyu da dubu dari biyar a lokacin da suke hanyar zuwa kasuwa domin sayawa yan bindiga babur.
Ya kara da cewa sun kuma kama harsashai, da tabar wiwi da layoyi da sihiri daga hannun wadanda aka kama.
A cewarsa, sauran wadanda aka kama sun hada da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, tare da kwato na’urorin hakar ma’adinai.
Dalijan ya bayyana cewa ‘yan sanda sun samu nasarar kama su a wasu sassan jihar Zamfara, Filato da Sokoto.
Ya ce sun yi aiki ne da sahihan bayanai da suka samu don cimma nasarar tare da yin kira ga mazauna yankin da su tallafawa hukumomin tsaro da muhimman bayanai.
Kwamishinan ya yi gargadin cewa gwamnatin tarayya da na jihar sun haramta hakar ma’adanai a fadin jihar don haka ya yi kira ga duk masu aikata wannan aika-aikar da su dakatar da yin hakan.
Your browser doesn’t support HTML5