Yaushe Za A Bayyana Sakamakon Zaben Shugaban Amurka?

Gwinnett County Voter Registration and Elections workers are already scanning ballots submitted in advance by mail-in and early voters.

Kada kuri’ar mutane kai tsaye zata kare ne da yammacin 5 ga watan Nuwamba inda kowane yanki zai tsayar da lokacinsa na dakatar da zabe.

Dalili shine jihohi nada dokoki mabambanta akan lokacin da za’a kirga kuri’u da kuma sanda za’a amince da kuri’un da aka aiko ta gidan waya, akwai yiyuwar wasu jihohin ba zasu san sakamakon ba har sai washe gari koma fiye da hakan.

Yin kankankan ma na baiwa kafafen yada labarai wahala wajen ayyana wanda ya lashe zabe da zarar an rufe rumfunar zabe.

Kamar yadda ya faru a 2020, da aka dauki tsawon kwanaki kafin a ayyana sakamakon zaben shugaban kasa, don haka akwai yiyuwar ba za’a iya sanin sakamakon manyan zabubbukan kasa ba, ciki harda na shugaban kasa har sai an shafe kwanaki bayan 5 ga watan Nuwamba.

Ya ya Ake Kirga Kuri’un?

Amurka ba ta da babbar hukumar zabe. Kowace jiha kan shirya irin tsarinta na kirga kuri’u.

Jami’an jihohi da na kananan hukumomi suna bada rahoton sakamakon zabe nan take, su kuma kafafen yada labarai sai su yi amfani da sakamakon, a akasarin lokaci da bayanan alkaluma, domin fayyace wanda ya lashe zaben.

Sau da yawa kafafen yada labarai kan sanar da wanda ya lashe zabe kafin kammala kidayar kuri’u ko jami’ai su sanarda sakamakon.

Dalili kuwa shine a kan dauki kwanaki ko makonni kafin a kammala kidayar kuri’u a gundumomi haka kuma sau da yawa, wani sashi na sakamakon ya wadatar a iya tantance wanda ya lashe zaben a lissafe.

Sai dai, duk lokacin da aka yi kankankan, kafafen yada labarai kan tsahirta wajen ayyana wanda ya lashe zaben har sai an bada sakamakon karshe.

Ba a fara bada rahoton sakamakon farko har sai an rufe rumfunan zabe a hukumance.

Yaya Ake Tabbatar Da Zaben?

Bayan an kammala kirga kuri’u, sai a tabbatar dasu a matakan kananan hukumomi da jiha. Sai jihohi su bayar da takardun da zasu tantance wakilan dake wakiltar dan takarar da ya lashe zaben jihar. A tsari, wakilai ‘yan jam’iyya ne ko kuma shugabannin jam’iyya ne ke nada su.

Za su yi taro cikin watan Disamba domin zaben shugaban kasa da mataimakinsa.

Daga nan sai sabuwar majalisar, wacce ke zama a watan Janairu, ta zauna domin kidaya sakamakon zaben sannan a bayyana wanda ya yi nasara a hukumance.

Daga nan sai a rantsar da shugaban kasa a wani bikin da zai gudana a ranar 20 ga watan Janairu.