Kogi Na Cikin Jihohin Dake Samar Da Danyen Mai - Ododo

Bututun mai

Ya koka a kan cewa duk da gano man da tarin yawa a Kogi, jihar ba ta cin gajiyar rabon kaso 13 cikin 100 da ake baiwa jihohin dake samar da danyen mai a Najeriya.

Gwamnan Kogi, Usman Ododo, ya bayyana cewar jihar na sahun jihohin dake samar da danyen mai sakamakon samun rijiyoyinsa da dama da aka yi a karamar hukumar Olamaboro ta jihar.

Sai dai, ya koka a kan cewa duk da gano man da tarin yawa a Kogi, jihar bata cin gajiyar rabon kaso 13 cikin 100 da ake baiwa jihohin dake samar da danyen mai a Najeriya.

Gwamna Ododo ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, a ofishinsa dake Abuja a yau Alhamis.

Ya bukaci samun goyon bayan ma’aikatar a kokarin da jihar Kogi ke yi na shiga sahun jihohin arewacin Najeriya dake neman a fara hakar mai a cikinsu.

A cewar Ododo, Kogi ce mahadar yankunan kudanci da arewacin Najeriya a aikin shimfida bututun iskar gas daya tashi daga Ajaokuta zuwa Kaduna ya zarce Kano (AKK), abin da ya bata babbar damar a harkar zuba jari a fannin mai da iskar gas.

A martaninsa, Lokpobori yace gwamnatin tarayyar Najeriya, ta hannun hukumar kula da cinikin albarkatun man fetur, na nazari a kan batun kasancewar Najeriya na bukatar karin danyen mai da iskar gas domin kara kudin shigarta, inda take harin fitar da ganga miliyan 5 a kowace rana daga ganga miliyan 2.5.