A DAWO LAFIYA: Matsalar Munanan Hanyoyin Mota A Jihar Neja a Najeriya - 12 Ga Watan Oktoba, 2024

Baba Makeri

Shirin na wannan makon ya mai da hankali ne akan matsalar rashin kyawun hanyoyin mota da ke ci gaba da jefa dubban al'umma cikin mawuyacin hali a jihar Nejan Nigeria.

Lamarin da ya sa yanzu haka, babbar hanyar da ta hada Minna zuwa Kontagora ta zarce zuwa Birnin Kebbi da sokoto da ma Jamhuriyyar Nijar suka rufe sakamakon faduwar wasu manyan motoci a dai dai garin Zungeru, wanda yasa ala tilas kananan motoci suka koma bin kan hanyar jirgin kasa da ta ratsa garin Kundu, lamarin dake da matukar hadari ga rayuwar al’umma.

A suarari sautin shirin tare da Baba Y. Makeri:

Your browser doesn’t support HTML5

A DAWO LAFIYA: Matsalar Hanyoyin Mota Mararsa Kyau A Jihar Nejan Najeriya Na Ci Gaba Da Jefa Dubban Jama’a Cikin Mayuyacin Hali