KALLABI: Tattaunawa Akan Hatsarin Tura Kananan Yara Mata Talla, Oktoba 6, 2024

Alheri Grace Abdu

Wannan makon shirin Kallabi zai haska fitila kan hatsarin tura kananan yara Mata talla da ake yi a kasashen da dama. Alkaluma na nuni da cewa sama kananan yara Mata miliyan 65 ne a fadin duniya basa zuwa makaranta, yayinda da dama daga cikin wadanda ke zuwa makarantar kuma basa yin nisa a karatu bisa dalilai daban daban.

Sannan Shirin zai kamala tattaunawa da Mama Sarah Jibril, mace ta farko da ta taba tsayawa takarar shugaban kasa a arewacin Najeriya.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

KALLABI: Tattaunawa Akan Hatsarin Tura Kananan Yara Mata Talla, Oktoba 6, 2024