Dattijon Arewacin Najeriya kuma tsohon hafsan hafsoshin Najeriya Janar Theophilus Danjuma mai ritaya ya bukaci shugabannin tsaron Najeriya su kawo karshen ‘yan bindiga sannan su dora kasar a kan turbar zaman lafiya. Babban janar din sojan mai ritaya ya koka da yawan sace sacen mutane da kashe kashe n da ake yi a arewacin kasar sannan ya ce, babu wata hujja da zasu bayar akan matsalar rashin tsaron da take neman yiwa kasar katututu.
Tsohon babban hafsan hafsoshin Najeriya-yace dole ne sojoji su kawo karshen matsalar tsaron da ake fama da su a Najeriya, ya ce basu da wata hujjar da zata hana su yin hakan.
Jawabin na Janar Danjuma ya zaburar da sojojin. Sai dai ga mai sharhi akan al’amuran tsaro kuma tsohon hafsan dakarun sojin saman Najeriya mai murabus Wing Commander Musa Isah Salmanu, ya ce sojojin Najeriya suna da kwarewar da zasu cimma wannan manufa har idan aka mai da hankali cikin dan kankanin lokaci.
Sai dai a nasa bangaren, masanin tsaro Dr. Kabiru Adamu, ya ce kamata yayi a duba matsayin soja a tsarin tsaro na kasa wanda yake da bangarori akalla 29 ko ma fi. Yace babu adalci a dora nauyin tsaron kasar baki daya akan hudu cikin bangarori 29 nan. Ya kara da cewa, dole ne sauran bangarorin suma su bada hadin kai don a samu a kawo karshen wannan matsalar.
Ya ce in ba a samu hadin kai da gudun mawar sauran bangarorin ba, to lallai babu yadda za ayi a shawo kan matsalar tsaron da ta zama ruwan dare a kasar.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5