Mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta soki alkawarin da dan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump ya yi na mai da miliyoyin mutanen da suke zama a Amurka ba bisa ka’ida ba, tana mai dora ayar tambaya akan ko zai dogara da yawan samamen da ake kai wa da inda ake tsare bakin haure ya cimma manufar sa ne.
Harris wace jam’iyyar ta Democrat ta tsayar a matsayin ‘yar takararta ta fada ma mahalarta babban taron makarantar koyar da aikin majalisa ‘yan asalin Hisfaniyawa na shekara shekara cewa kasar za ta iya lalubo hanyoyin da za abi don bakin haure su samu damar zama ‘yan kasa ga wadanda suke sha’awar shigowa kasar sannan a lokaci guda kuma a tabbatar da tsaro a kan iyaka.
Ta ce “Zamu iya yin duka biyun kuma dole ne ma muyi duka biyu,”.
A nashi bangaren kuma, Trump ya fi karkata akan jan hanlakin da yake yi akan shige da fice, yayin da ya yi gangamin zabe a Uniondale dake gabar tekun Long Island a birnin New York, inda ya fi mai da hankali akan kalaman sa akan batun.
Abin da mu ke yi shi ne lalata ginshikin rayuwar kasarmu. Kuma ba za mu ci gaba da amincewa da hakan ba. Sannan akwai bukatar mu kore wadannan mutanen. Trump ya ce, Ku ba ni dama.
Dukkanin ‘yan takarar sun dan dakatar da gangamin yakin neman zabe a jihojin da za su iya zama manuniya ga wanda zai yi nasara a zaben ranar 5 ga watan Nuwamba a ranar Laraba. Tsohon shugaban kasa Donald Trump ya samu goyon bayan mutane da dama da suke ta shewa, inda suka ba shi dama ya bayyana wa ‘yan jihar goyon bayan shi.
Ya caccaki shugabancin jam’iyyar Democrats a birnin New York da jihar yana mai dora mu su laifin matsalar mutanen da ba su da matsuguni, lamarin da ya ayyana da abin takaici mai ban kyama, mai hadari, matsugunai mara kyau sannan kuma akan yanayin abubuwan da ke faruwa a tashar jiragen kasar birnin na New York, wanda ya ayyana da mara kyau mai tattare da hadari, kuma yayi alkawarin gyara lamarin.