An Zabi Dan Najeriya Domin Fafatawa Wajen Lashe Kyautar Ballon D’or Ta Bana

FBL-CAN-2024-NGR-ANG

An zabi dan wasan gaban Super Eagles, Ademola Lookman, domin fafata wajen lashe kyautar dan kwallon kafa mafi bajinta a bangaren maza ta bana mai lakabin ballon d’or.

Sunan dan wasan mai shekaru 26 dake taka leda a kungiyar Atlanta ta kasar Italiya ya fito cikin jerin sunayen ‘yan wasa 29 da zasu fafata wajen lashe kyautar da mujallar kwallon kafar kasar Faransa ta wallafa a jiya Laraba.

Lookman ne dan wasa daya tilo daga nahiyar Afirka dake cikin jerin sunayen.

Ba’a sanya sunan dan wasan daya taba lashe kyautar har sau 8 kuma har yanzu yake rike da kabunta Lionel Messi a cikin jerin sunayen na bana ba, haka shima wanda ya taba lasheta har sau 5 Cristiano Ronaldo

Lookman na cikin karsashi kasancewar kungiyarsa ta atalanta ta lashe kofinta na farko a gasar nahiyar turai a kakar data gabata, inda dan najeriyar ya dura kwallaye 3 rigis a wasan karshe na gasar europa a ragar bayer leverkusen.

Ya ciwa atalanta jumlar kwallaye 17 tare da taimakawa a ci 11 a kakar da ta gabata.

wasu daga cikin fitattun ‘yan wasan dake cikin jerin sunayen sun hada da Jude Bellingham da Vini Junior da Erling Haaland da kuma Kylian Mbappe.