An Tsaurara Tsaro A Gasar Olympics Bayan Zagon Kasar Da Aka Yiwa Jirgin Kasa

Wata majiya dake kusa da binciken da ake gudanarwa a kan lamarin ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa hare-haren wani tsararren al’amari ne na yin zagon kasa”

A yau Juma’a, tsarin sufurin jiragen kasan Faransa mai tsananin gudu ya gamu da “mummunar barazana” ciki har da tashin gobarar da ya hargitsa al’amura, a cewar kamfanin SNCF dake gudanar da harkar, ‘yan sa’o’i gabanin fara bukukuwan bude gasar olympics ta birnin Paris.

Wata majiya dake kusa da binciken da ake gudanarwa a kan lamarin ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa hare-haren wani tsararren al’amari ne na yin zagon kasa”, inda ya kara da cewa ya zama wajibi a soke tafiye-tafiyen jirgin kasan da dama.

A cewar kamfanin dake gudanar da harkar sufurin jiragen kasan kasar Faransa, “munanan hare-hare da dama sun afka wa SNCF a cikin dare”, inda ya kara da cewa hare-haren sun fi shafar layin dogon da ya ratsa tekun Atlantic da wadanda suka nufi yankunan arewaci da gabashin kasar.

Sanarwar da kamfanin ya fitar tace, “an karkatar da jiragen kasa zuwa wasu layukan dogon na daban, amma ya zama wajibi a soke da dama daga cikinsu.”

Layin dogo na kudu maso gabashin kasar ya tsira kasancewar “an yi nasarar dakile wani mummunan hare.”

Kamfanin na sncf ya shawarci fasinjoji su dage tafiye-tafiyensu tare da kauracewa tashoshin jiragen kasa.