Ana Ci Gaba Da Kokarin Ceto Mutanen Da Zaftarewar Kasa Ta Rutsa Da Su A Kasar Habasha

  • Murtala Sanyinna

Zaftarewar kasa a Habasha

An ci gaba da kokarin ceto mutane har ya zuwa yammacin jiya Talata a yankin Gofa, bayan zaftarewar kasa yayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 229 a kudancin kasar Habasha.

Adadin na wadanda suka mutu ya hada da mutane da dama da kasa ta binne su a ranar Litinin, a yayin da ma’aikatan ceto suka karade yankin domin ceto masu sauran rai daga wata zaftarewar kasa a ranar Lahadi, a cewar hukumomin kasar.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne suka haddasa zabtarewar kasar a gunduma mai nisa ta Kencho Shacha Godzi ta kasar Habasha.

Zaftarewar kasa a Habasha

Daga cikin wadanda suka mutu har da kananan yara da mata masu juna 2, a cewar wani jami’in yankin, ya kara da cewa an sami zaro mutane akalla 5 da ran su.

Firai Minista Abiy Ahmed ya ce an tura jami’an hukumar kula da bala’o’i ta kasar zuwa yankin, domin taimakawa wajen aikin bincike da ceto.