A hirar shi da ma’aikacin tashar talabijin ta NBC Laster Holt, Biden yace, "Kuskure ne yin amfani da kalmar, Ina nufin mayar da hankali a kai, mayar da hankali ga abin da yake yi,"
A ranar 8 ga watan Yuli, Biden, mai shekaru 81, ya yi jawabi ga wasu manyan masu ba da gudummawa a yakin neman zabensa, ya kuma ce suna bukatar su kauda hankalinsu a yakin neman zaben daga kanshi da kuma rashin taka rawar gani a mahawararsa da tsohon shugaba Trump, dan takarar Republican a zaben na ranar 5 ga Nuwamba.
Ya ce, "Ina da aiki daya kuma shine in doke Donald Trump ... Mun gama magana game da muhawarar. Lokaci ya yi da za mu sanya Trump a “gaba” in ji shi.
Wadansu 'yan jam'iyyar Republican sun yi watsi da wannan tsokaci yayin da suke zargin Biden da haifar da yanayin yunkurin kashe Trump a wani gangami a Pennsylvania ranar Asabar. Biden ya sha yin tir da tashin hankalin siyasa.
Shugaba Biden, ya yi kokarin ganin an maida hankalin kan abokin hamayyarsa, inda ya ambaci karairayin Trump, da kin amincewa da sakamakon zaben 2020 da Trump ya yi, da kuma rawar da ya taka a harin da aka kai a ranar 6 ga watan Janairun 2021 a babban birnin tarayya.
"Ni ba mutumin da ya ce ina son zama dan kama-karya tun daga ranar farko ba. Ba ni ne mutumin da ya ki amincewa da sakamakon zaben ba," in ji Biden.
Ya ce Trump ya na yin kalamai masu tada hankali, inda ya ba da misali da kalaman tsohon shugaban kasar kan zubar da jini da zai biyo baya idan ya fadi zaben 2024, da kuma yin dariya a lokacin da wani mai kutse ya kai wa Maigidan tsohuwar kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi, Paul hari da guduma a gidansu.