Ranar samun ‘yancin kai, wacce aka fi sani a magance da 4 ga watan yulin kowace shekara, ranar hutu ce a tarayyar Amurka da ake bikin zartar da kudirin ayyana samun ‘yancin kan da aka aiwatar a ranar 4 ga watan Yulin, 1776, abinda ya samarda dunkulalliyar kasar Amurka.
Wakilan Majalisar sun ayyana cewar yankuna Amurka 13 basa karkashin ikon Sarkin Ingila na wancan lokacin, Sarki Joji na 3, kuma sun dunkule a wuri guda, sun zama ‘yantattun jihohi.
Majalisar sun kada kuri’ar amincewa da samun ‘yancin kai ta hanyar zartar da kudirin da ake yiwa lakabi da “Lee Resolution” a ranar 2 ga watan Yuli sa’annan suka zartar da kudirin ayyana samun ‘yancin a ranar 4 ga watan Yuli.
Ana gudanar da bukukuwan samun ‘yancin kan ne ta hanyar wasannin tartsatsin wuta da fareti da gashe-gashen nama da kalankuwa da baje koli da shakatawa da wake-wake da raye-raye da wasannin kwallon baseball da ziyartar dangi da jawaban siyasa da bukukuwa, baya ga tarurrukan al’umma dana daidaikun jama’a domin murnar kafuwar tarihi da gwamnati harma da al’adun dunkulalliyar Amurka.