Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya shaidawa gwamnatin jihar Sokoto cewar wajibi ne a girmama Mai Alfarma Sarkin, Muhammad Sa'ad Abubakar, iya girmamawa .
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a taron kolin zaman lafiya da tsaro a jihohin arewa maso yammacin Najeriya dake gudana a jihar Katsina da ake yadawa kai tsaye a tashar talabijin ta Channels.
A cewarsa "ga Mataimakin Gwamnan Sokoto, ina da dan sakon da zan baka. eh! na yarda ana cewa Sarkin Musulmin Sokoto, saidai martabarsa ta zarta hakan, shi sarki ne dake wakiltar akida. Shi wata hukuma ce daya kamata dukkaninmu a kasar nan mu martaba iya martabawa tare da bashi kariya da bunkasawa da alkintawa da kuma tallata mutuncinsa a idon duniya.
A safiyar yau ne kungiyar da ke rajin kare hakkin Musulmi ta Najeriya (MURIC) ta bayyana damuwa game da zargin cewar gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu na shirin tube Sarkin Musulmi.
"MURIC ta baiwa gwamnan shawarar cewar ya duba kafin ya sara. Kujerar Sarkin Musulmi ta zarta ta al'ada. Kujera ce ta addini. Kuma hurumin sarkin ya zarta Sokoto. Hurumi ne daya karade fadin Najeriya. Shine jagoran addinin ilahirin Musulmin kasar."
Don haka duk gwamnan daya kuskura ya taba alfarmar kujerar Sarkin Musulmi, toh, gashi nan ga Musulmin Najeriya saboda bayan mukamin Sarkin Musulmi kuma shine Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, a cewar Akintola.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin al'amura da cece-kuce ke kara kamari game da raba wasu sarakuna da kujerunsa da aka yi a jihar Kano.
A baya gwamnan Sokoto Ahmad Aliyu ya sauke wasu sarakuna 15 daga kan kujerunsu akan dalilai daban-daban.
Ku Duba Wannan Ma Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Tube Wasu Sarakuna Da Ta Zarga Da Taimaka Wa Ayyukan Ta’addanciHar yanzu gwamnatin jihar Sokoto bata ce komai ba game da zargin na kungiyar MURIC, saidai a baya tace akwai shirye-shiryen yin gyara akan sashe na 79 na dokar kananan hukumomi da harkokin masarautun jihar domin tayi daidai da al'adun jihar.