Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan kudiri da hadakar majalisar dokokin Najeriya ta zartar kan komawa tsohon taken kasar ta “Nigeria, we hail thee” a turance.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya tabbatar da hakan yayin zaman hadakar majalisar a yau Laraba.
Sanata Godswill Akpabio ya kara da cewa zaman Majalisar ta yau ta musaman ce saboda tabbatar da komawa tsohon taken na ''Nigeria, we hail thee" a turance.
Sai dai yace Shugaba Tinubu ba zai gabatar da jawabi ba kamar yadda ake zato saboda zai halarci bikin kaddamar da shirin 'Abuja Metro Line'.
Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai a lokuta daban-daban suka zartar da kudirin komawa tsohon taken Najeriya cikin mako daya.
An maye gurbin tsohon taken daya soma da "Nigeria, we hail thee" a turance da wanda ya soma da “Arise o' compatriots" a shekarar 1978.
Tsohon taken da aka kirkira lokacin da Najeriya ta samu 'yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban 1960 zai maye gurbin wanda ake amfani dashi a halin yanzu.
Manufar kudirin shine sake farfado da tsohon taken da aka yi watsi dashi a 1978 lokacin gwamnatin mulkin sojan Olusegun Obasanjo.
Wani bakon haure dan asalin Burtaniya daya zauna a Najeriya mai suna Jean Williams ne ya rubuta taken na "Nigeria, we hail thee " .