Yayinda da yake yanke hukuncin a ranar Juma’a, alkalin kotun, Mai shari’a Emeka Nwite ya ce, kotun ta ki amincewa da bukatar na neman belin ne bayan da ya yi nazari a kan takardun.
Yayinda a halin da ake ciki, mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilai kan dokokin da aka wakilta, Dominic Okafor, ya musanta zargin kabar cin hancin dalar Amurka miliyan 140 daga manyan shugabannin kamfanonin hada-hadar Kudi ta Yanar gizo Binance.
Okafor, wanda ya yi magana da manema labarai a harabar majalisar dokokin tarayya, Abuja ranar Juma’a, ya yi barazanar daukar matakin shari’a a kan wata kafar yada labarai ta yanar gizo da ta wallafa labarin.
Gwamnatin Najeriya dai na tuhumar dandalin Binance da zarge-zargen kaucewa biyan haraji guda 4.
Ku Duba Wannan Ma Kotu Ta Tura Jami’in Kamfanin Binance Kurkukun Kuje Ku Duba Wannan Ma Gwamnatin Najeriya Ta Musanta Zargin Neman Cin Hancin Dala Miliyan 150 Daga Kamfanin BinanceHukumar Tattara Kudaden Haraji ta Tarayya (FIRS) ta sanar da hakan, inda tace an shigar da tuhume-tuhumen ne a hukumance gaban babbar kotun Abuja.
Tuhume-tuhumen da ake yiwa Binance sun hada da zargin: kin biyan harajin VAT da ake caza akan kowace hada-hada da wanda ake biya akan gudanar da kamfani da kaucewa bayar da bayanai akan harajin da kamfani ya kamata ya biya da kuma yin amfani da dandalin wajen taimakawa abokan huldarsa su kaucewa biyan haraji.
A cikin kunshin wadanda ake tuhuma tare da Binance din akwai Shugabannin Kamfanin; Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla da yanzu haka ya tsere daga hannun Hukumar EFCC me yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati.