Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya fara share fagen nemawa kananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kansu domin dakile matsalolin rashin tsaro da kaura daga kauyuka zuwa birane da lalacewar ababen more rayuwa da karuwar matsalar rashin aikin yi.
Majalisar Dattawan ta kuma nemi Shugaba Tinubun ya shirya taron kasa da zai kunshi gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da jami’an kananan hukumomi harma da shugabannin al’umma domin tattaunawa akan hanyar da za’a bi wajen tabbatar wa kananan hukumomi da cikakken ‘yancin cin gashin kai.
Wasu ‘yan majalisar, da suka bayyana kananan hukumomi a matsayin matakin gwamnatin da aka fi ciwa zarafi, sun bukaci a yiwa kundin tsarin mulkin najeriya na 1999 wadda aka yiwa kwaskwarima domin tabbatar da wannan ‘yanci.
Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawan, Sanata Abba Morro, yayi tsokacin cewar yau fiye da shekaru 17 kenan ana gudanar da tsarin kantomomi a kananan hukumomin Najeriya, abinda ya haifar da karan tsaye ga tsarin gudanarwar kananan hukumomin.
Ya cigaba da cewar kada ayi kasa a gwiwa har sai an bankado irin cin zarafin da aka yiwa tsarin kananan hukumomin.
Shima Sanata Ifeanyi Ubah, dake wakiltar mazabar Anambra ta Kudu a majalisar dattawan, yace jiharsa bata gudanar da zaben kananan hukumomi ba a shekaru 18 din da suka gabata.
Ya kara da cewar rashin aiwatar da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin 1999 ne ya kawo babban cikas ga samun ‘yancin kananan hukumomi.