Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yanke Hukuncin Daurin Rai Da Rai Ga Dan Najeriya Da Ya Kashe Matarsa A Ingila


Taiwo ta rasu ne a watan Nuwamban shekarar 2023 sakamakon mumunan raunin da ta samu a kwakwalwar ta bayan afkuwar mumunan lamarin a gidan su da ke Newmarket.

Wani dan Najeriya mazaunin Ingila Olubunmi Abodunde, mai shekaru 48 a duniya da ya kashe matarsa Taiwo, da wani abin wasan dansa, ya gamu da daurin rai da rai a gidan kaso.

Olubumin ya kuma dora alhakin aikata hakan kan wani magani da yake sha, da kan sa ya kasa rike kansa.

Taiwo ta rasu ne a watan Nuwamban shekarar 2023 sakamakon mumunan raunin da ta samu a kwakwalwarta bayan afkuwar lamarin a gidansu da ke Newmarket.

Kafaffen yada labaran Ingila sun ruwaito cewa, ya tabbatar da kisan matarsa, wadda ta samu mumunan rauni a kwakwalwa.

Irin munin harin da ya kai mata a gidansu dake kan titin Exning ya haifar mata da jin ciwon da yayi sanadiyyar mutuwarta, kamar yadda kotun Ipswitch Crown ta lura.

Abondunde ba zai sami damar fita daga kurkuku ba a wucin gadi har sai bayan shafe shekaru 17 a daure.

An sanar da kotun cewa, an kama Abodunde ne biyo bayan wani al’amarin makamancin wannan da ya faru kwana guda kafin mutuwarta.

An haramta masa ganawa da iyalinsa, a matsayin sharadi daga cikin sharuddan sakin sa daga caji ofis.

Duk da sharadin, a washegari sai da Abodunde ya je gida da niyar daukan wayarsa ta salula.

Taiwo, uwar ‘ya’ya uku kuma ma’aikaciyar kiwon lafiya, ta dawo da ga aikin dare ne a ranar da lamarin ya faru.

Mai gabatar da kara Stephen Spence KC, ya shaidawa kotun cewa, Abodunde na sane sarai da yadda tsarin aikin matarsa yake, kuma kyamarar CCTV ta nuna Taiwo ta dawo gida da misalin karfe 9 da mintuna 12 na tsafe agogon GMT.

Abodunde dai ya yi ta zub da hawaye a kotu lokacin da ake zayyano irin akubar da matarsa ta sha kafin da ga bisani rai yayi halin sa.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG