A safiyar yau juma’a 1 ga watan Maris ne kwamandan Hisbah Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana ajiye aikinsa na shugaban hukumar a shafinsa na Facebook biyo bayan rashin samun goyon bayan wajen gudanar da ayyuka akan ayyukan kauda badala.
Malamin ya bayyana saukarsa ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook inda yake cewa a halin da ake ciki suna jihar Kaduna inda suke tattaunawa da yan majalisa domin lalubo hanyar sanya dokar gudanar da gwaji na Lafiya kafin aure.
Ya ce yana can ne ya samu bayyanai daga Kano wanda suka kashe masa gwiwa dangane da yunkurin da hukumar ta Hisbah ke gudanarwa na kauda badala.
Daurawa ya ce "Mun yi iya ƙoƙarinmu domin yin abin da ya kamata, to amma ina bai wa mai girma gwamna haƙuri bisa fushi da ya yi da maganganu da ya faɗa. Kuma ina roƙon ya yi mani afuwa na sauka daga wannan muƙami da ya bani na shugabancin Hisbah."
Gwamna Abba Kabir dai ya bayyana rashin jin dadinsa ne ga yadda hukumar Hisbah ke gudanar aikin kame na kau da badala a jihar ta Kano.
Gwamna Abba ya bayyana hakan ne a jiya a wani taron na tataunawa da limamai a gidan gwamanti, inda ya nuna damuwarsa na yadda ake gudanar da samamen kau da badala.
Mal Daurawa ya ce tun ya fara aikinsa ya gana da yan masana’antar Kannywood , da yan TikTok wanda shi da sauran yan hukumar ta Hisbah, suka hada kudadensu domin gayyatarsu tare da ba yan TikTok din kudin mota da na data duk a yunkurin magance rashin tarbiya.