Fitaccen mai shirya fina-finan nan Tyler Perry ya dakatar da shirinsa na kashe dala milyan 800 wajen fadada wurin harhada fina-finansa dake jihar Atlanta Georgia.
Tyler Perry ya shaidawa dan jaridar dake daukar rahotannin masana’antar shirya fina-finan Hollywood cewar, mutum-mutumin Sora da aka fara amfani dashi a ranar 15 ga watan Fabrairun da muke ciki zai iya aikata wadannan al’amura wani abu ne daban, amma ganin zahirin bajintar daya aikata ta tafi da tunanina.”
Perry, wadda Netflix ya fara haska wani fim dinsa mai suna, “Mea Culpa” a Juma’ar data gabata, yace aikin fadada wurin harhada fina-finan na iya samar da karin matakan fidda sauti guda 12.
"Saidai yanzu dukkanin wannan ya tsaya chak,” shawarar kenan da Perry ya yanke a matsayin martani ga irin tasirin da basirar mutum-mutumin Sora za ta iya yi akan harkar shirya fina-finan a yadda take a halin yanzu.
Perry, na hangen wani yanayi da zai sanya shirin daukar fim a dandali ko wani gini ya zamo tarihi.
A cewar Perry, mun sha tattaunawa akan batun a shekarar data gabata, cewar al’marin nan na zuwa, saidai ban fahimta ba har sai dana kalli gwajin irin bajintar da zata iya samarwa. al’amarin yayi matukar ban mamaki.”