Shugaban Kwamitin Amintattu na Gamayyar Kungiyoyin Arewa, Alhaji Nastura Ashir Sharrif ya ce rashin manhaja na bai daya da jami'an tsaro za su yi amfani da shi na cikin ababen da ke hana magance matsalar tsaro da arewacin Najeriya ke fama da shi.
Alhaji Sharrif ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da Muryar Amurka, a birnin Abuja, in da ya ce hakan ne ya sa Kungiyar ta kira wani taron gaggawa a kan harkokin tsaro bayan nazari na tsawon sama da watanni 4.
Yace sun yi muhawara na musamman a kan ababen da suka jawo yadda aka shafe tsawon shekaru sama da 10 ba’a iya magance su ba.
A cewar Alhaji Nastura, nazarin nasu ya gano muhimman abubuwa 4 da suka hana magance matsalar.
Ya ce "tun da aka fara yaki da matsalolin tsaro kama daga kan matsalar mayakan boko Haram, gwamnatin tarayya bata da manhaja na bai daya ga rundunonin tsaro, kamar na yan sanda, sojojin sama, kasa da na ruwa, hukumar DSS da dai sauransu wanda baki daya a kan ta suke yaki.
"Na biyu, ana samun rashin fahimta tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi, mafi muni a ciki kuma shi ne rashin sanya al’umma a cikin rigimar wannan yaki da ‘yan ta’adda. Su kuma al’umma basu yi tunani a bisa kashin kansu. Su koma da baya su je kowa a iya matakin da yake ya fara daukan wasu tsari da zasu kawo karshen wannan tsarin", in ji Nastura.
Gamayyar kungiyoyin Arewar dai tace zata fara hada gwiwa da al’umma don bada gudunmuwar kawo karshen matsalolin tsaron da taimakon al’umma.
Ga cikakken bidiyon hirar da wakiliyar Muryar Amurka, Halima Abdulrauf, ta yi da shi.
Your browser doesn’t support HTML5