Mai Shari’a Hamza Mu’azu na babbar kotun birnin tarayyar Najeriya, Abuja ya amince da bukatar tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ta yin balaguro zuwa wajen birnin Abuja.
Saidai a cewar kotun, wajibi ne Emefiele ya ci gaba da kasancewa a cikin kasar. Sharuddan bada belinsa, sun takaita zirga-zirgarsa zuwa kwaryar birnin Abuja.
Emefiele, ta hannun lauyansa, Mathew Burka, ya bukaci a sauya sharudan.
Lauyan hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Rotimi Oyedepo bai kalubalanci bukatar ba.
Sai dai ya bukaci kotun ta tabbatar Emefiele ya rubuta yarjejeniyar ci gaba da kasancewa a cikin Najeriya matukar aka amince da tasa bukata.
An kuma kara yawan tuhume-tuhumen da ake yiwa tsohon gwamnan zuwa 20 daga guda 6.
Sabbin tuhume-tuhumen da ake yiwa emefiele sun hada da cin amanar kasa da yin takardar bogi da hadin baki domin yin takardun bogi da badakalar bada kwagila da kuma hada baki wajen aikata laifi.
A ranar 24 ga watan Disambar shekarar 2023, aka bada belin Emefiele akan kudi naira milyan 300 da mutum 2 da zasu tsaya masa akan milyan 300 kowannensu.
Lauyansa wanda kwararre ne ya shaidawa tashar talabijin ta Channels cewar an saki Emefiele daga gidan gyaran hali na Kuje bayan da lauyoyinsa suka cika dukkanin sharudan bada beli.
An gurfanar da Emefiele ne a bisa tuhume-tuhume 6 da ke da nasaba da yin zamba wajen bada kwangila ta hanyar yin amfani da mukaminsa wajen ba wa wata ma’aikaciyar Babban Bankin Najeriya mai suna Sa’adatu Yaro haramtacciyar dama, inda ya bata kwangilar sayen motoci 43 da kudinsu ya kai naira bilyan 1 da milyan 200 tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.
Ka cikakken rahoton Halima Abdulrauf
Your browser doesn’t support HTML5