AREWA A YAU: Bitar Wasu Daga Darussan Da Shirin Ya Tabo a Shekarar 2023, Kashi Na Karshe - Janairu 17, 2024

Nasiru Adamu El-Hiyaka Lokacin Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Sabon shirin Arewa a Yau, shi ne na karshe a jerin dukkan shirye-shirye 144 da mu ka gabatar kan lamura daban-daban da su ka shafi arewa musamman kalubalen tsaro, kuncin tattalin arziki da rabuwar kawuna.


A yayin da Muryar Amurka ke cika shekaru 45 da fara aiki ta bullo da sabbin shirye-shirye da za su maye gurbin wasu shirye-shiryen da su ka hada da wanann shirin.

Za mu kammala shirin da jan hankali da mai bishara na addinin Kirista, Fasto Yohanna YD Buru, ya yi kan yiyuwar cikawa ko saba alkawarin da 'yan siyasa kan dauka wa 'yan arewa.

Daga nan za mu yi bitar sharhin tsohon gwamnan Sokoto Aattahiru Dalhatu Bafarawa kan tsaro a Arewa da ya yi gargadi a 2002 a gidan Arewa a Kaduna cewa matukar ba a hada kai ba, allura za ta tono garma.

Tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa ya duba tsokaci da ya yi a 2002 har ma gargadin ya zama littafi inda daga bisani fitinar Boko Haram ta shigo yankin daga 2009 sannan a 2015 matsalar barayin daji ta fara gawurta daga barayin shanu.

Saurari shirin a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

AREWA A YAU