Mai shari’a John Okoro, wanda ya karanta hukuncin, ya ce kotun daukaka kara ta yi kuskure wajen tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke, inda ta ce Yusuf bai samu mafi rinjayen kuri’un da aka kada a zaben gwamnan jihar Kano da aka yi ranar 18 ga Maris na shekarar 2023 ba.
A yayin da take yanke hukunci, kotun kolin ta tabo batutuwa biyu da suka hada da ko karamar kotun ta yi daidai wajen cire kuri’u dubu 165 da 616 daga cikin kuri’un da hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta sanar da Abba Kabir a Matsayin gwamna da kuma ko karamar kotun za ta iya tantance batun zama mambobin jam’iyya.
A hukuncin da kotun ta zartar, Mai shari’a Okoro ya ce karamar kotun ta yi kuskure wajen cire kuri’u dubu 165 da 616 daga cikin wanda aka kada wa Abba Kabir Yusuf a zaben bisa hujjar cewa jami’an INEC ba su sanya hannu da tambari a takardun kuri’un ba.
A cewar sa, sashe na 71 na dokar zaben da kotun ta dogara da shi wajen cire kuri’un da ake cece-kuce a kai ba ya aiki kai tsaye ko cikin gaggawa.
Daga bisani kotun koli ta alkalai biyar ta yi gaba da mayar da kuri’u dubu 165 da 616 da aka cire don dawo da nasarar Yusuf a zaben gwamnan jihar Kano.
A batu na biyu, kotun kolin ta sake caccakar kotun daukaka kara da cewa Yusuf ba dan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da ya tsaya takara, inda ta kara da cewa batun nadawa da daukar nauyin zabe abu ne na gabanin zabe kuma ba hurumin kotun bane.
Mai shari’a Okoro ya lura cewa sabanin matsayin kotun daukaka kara, kotun sauraron kararrakin zabe ba ta taba cewa Yusuf bai cancanci tsayawa takara ba saidai ba bu sunansa a cikin rajistar mambobin jam’iyyar NNPP da aka mika wa hukumar INEC.
Daga nan ne kotun kolin ta yi watsi da hukuncin da kananan kotunan biyu suka yanke kan rashin gaskiya da kuma mayar da nasarar Abba Yusuf a zaben.