Ministan ta bayyana hakan ne sa’ilin data ziyarci asibitin dake abuja a ranar talata.
A cewarta takai ziyarar ne domin tallafawa shahararren jarumin, da yi mishi fatan samun sauki tare da mika sakon fatan alkhairi daga gwamnatin tarayya ga shi da iyalansa.
“Wannan bawan all.h ya sadaukar da lokaci da basira domin ya samu dariya da nishadantar da ‘yan Najeriya tsawon lokaci.
“Yana daga cikin mutanen da suka aza harsashin ginin masana’antar fina-finan Najeriya kuma gashi an yi rashin sa’a yana fama da kalubale na lafiya harma anyi mishi tiyata a kwakwalwa.
“Iya abinda zamu iya yi a matsayinmu na gwamnati shine bashi tallafin da ya dace domin tabbatar da ya samu waraka cikin sauri”, in ji Ministan.
Ta kara da cewa “tiyatar kwakwakwa abu ne mai wahalar gaske, don haka yana da mahimmanci a "matsayi na ta Ministar Fasaha, Al’adu da Bunkasa Tattalin Arziki ta Hanyar Kirkira in ziyarce shi”, in da ta bukaci ‘‘yan najeriya su taimaka mishi da addu’a da duk abinda za su iya domin tallafa masa da iyalinsa wajen ceto rayuwarsa”.
Musawa ta ci gaba da cewar gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta fahimci mahimmacin da fannin fasaha ke da shi wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, kuma ta dukufa wajen tabbatar da walwalar masu ruwa da tsaki a harkar.
A cewarta, ma’aikatar raya al’adu karkashin kulawarta na aiki tukuru wajen bijiro da shirye-shirye da tsare-tsaren tabbatar da jin dadin masu ruwa da tsaki a fannin.
Musawa, wacce ta bada gudunmowar adadin kudin da ba’a bayyana ba domin biyan kudin asibitin jarumin dake jinya, tace akwai kyakkyawan fata a fannin kirkira da fasahar Najeriya.
“Guda da ga cikin mahimman abubuwan da muka bijiro da shi a ma’aikatarmu shi ne tabbatar da walwalar, ba wai ga iya jaruman da suka yi shura ba, harma da ilahirin mambobin masana’antar shirya fina-finan”.
Rahotanni sun bayyana cewar an kwantar da Zack Orji mai shekaru 64 a sashen Kulawar Musamman na Asibitin Kasa dake Abuja bayan da ya yanke jiki ya fadi a jajibirin sabuwar shekara, kafin daga bisani a maida shi zuwa wani asibiti mai zaman kansa.