Gwamnatin Najeriya ta fito karara ta ce za ta hukunta duk wanda ta samu da hannu a harin bam din jirgi marar matuki kan jama'ar Tudun Biri a jihar Kaduna matukar an gano akwai ganganci a harin.
Ministan labarun Najeriya Muhammad Idris Malagi ne ya ba da tabbacin a jawabinsa ga manema labaru na karshen shekrara nan ta 2023.
"Mu na kara jajantawa al'ummar Tudun Biri kan wannan akasin da ya faru kuma gwamnati na daukar matakan bincike kan yadda harin na jirgi marar matuki ya auku." In ji minista Muhammad Idris.
Ministan ya fito karara ya ba da tabbacin daukar matakai kan masu sarrafa jirgin musamman in an gano sakaci ko ganganci.
"Ba ta yadda gwamnati za ta bari a yi irin wannan laifi ba ta hukunta wanda a ka samu da laifi ba." Ya ce.
Ya kara da cewa gwamnati na tattaunawa don karawa ma'aikata albashi a shekarar 2024 mai shigowa, yana mai cewa duk 'yan Najeriya za su amfana daga ribar cire tallafin man fetur da hakan ya janyo kuncin rayuwa.
Ministan ya yi bitar muradun gwamnatin Tinubu guda takwas da ya sa a gaba ciki har da farfado da tattalin arziki, inganta tsaro, sufuri, lafiya da sauran su amma ba a ambaci yaki da cin hanci ba.
Hakan ya zama ya sha bamban da irin muradun tsohon shugaba Buhari wanda an cimma ko ba a cimma ba bayanai za su tabbatar.
Dattawa 'yan siyasa irin Hussaini Gariko na son lalle gwamnati ta sake sauya dabara matukar za ta yi wani tasiri.
Shugaba Tinubu na cewa yana jin irin zafin kuncin da 'yan Najeriya ke ji amma Hausawa kan ce da fama da tsiya gara da arziki.
Saurari Nasiru Adamu El Hikaya da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5