Misalin irin wadannan korafe-korafe sun hada da wasikar kungiyar SERAP mai rajin tabbatar da dai-daito a Najeriya ta ranar 25 ga watan Fabrairun bana ga shugaban Amurka Joe Biden, kan neman Amurkan ta hana biza da kuma kwace kadarorin ‘yan siyasa masu dabi’ar kitsa magudi da ta da fitina a zabukan da Najeriya ta yi a bana.
Kazalika, shi ma tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya a jihar Osun Barrista Kanmi Ajibola, ya rubuta makamanciyar wanna wasika a ranar 16 ga watan Disambar 2019 ga kungiyoyin da ECOWAS da kuma Majalisar Dinkin Duniya, ya na neman su takawa shugaban Najeriya na wancan lokaci birki Muhammadu Buhari, kan zargin rashin mutunta umarnin kotunan kasar.
Bugu da kari korafi na baya bayannan shi ne wanda reshen jihar Kano na Jam’iyyar NNPP ya rubutawa kungiyar ta Tarayyar Turai EU da gwamnatin Canada da ma Majalisar Dinkin Duniya game da dambarwar shari’ar gwamnan Kano da ke gaban kotun kolin Najeriya.
Farfesa Kamilu Sani Fagge masanin kimiyyar siyasa daya kware a fannin diflomasiyya ya ce, “tasirin wadannan kungiyoyi da hukumomi na kasashen waje ga siyasar duniya, da kuma alakarsu da shugabannin kasashen masu korafin shi ke karfafa gwiwar masu rubuta irin wadannan wasiku, amma haka ba ya tasiri sosai, saboda su wadannan hukumomi da kungiyoyi na ketare ba sa son yin katsalandan akan harkokin cikin gida na kasashen duniya”.
Sai dai galibin marubuta irin wadannan wasiku na ganin mataki ne da ya dace tun da magana ake ta dimokaradiyya, kuma wadannan kungiyoyi suke tallata dimokaradiyyar duniya.
Amma Dr. Abbati Bako, mai ilimin falsafar siyasar duniya na cewa ya yi, “ba na zaton akwai wata kungiya ko hukuma ta duniya da za ta iya shiga harkokin shari’a na cikin gidan wata kasa, saboda kowace kasa tana da tsari na yadda shari’arta take tafiya”.
Ga alama, bakin masana ya zo wuri guda kan rauni ko rashin tasirin irin wadannan wasiku da akan rubutawa kungiyoyi da hukumomin ketare, saboda babu tabbacin suna ba da amsa ba ga marubuta wasikun.
Your browser doesn’t support HTML5