Wani fim din Najeriya da ya ba da labari kan matsalar cin hanci da rashawa da cin zalin da ake zargin ‘yan sanda na yi a kasar wacce ta fi yawan al’uma a nahiyar Afirka, ya taka wani muhimmin mataki na yawan wadanda suka kalli fim din a dandalin fina-finai na Netflix a duk duniya.
Wannan wata alama ce da ke nuni da bunkasa da masana’antar fina-finan ta Najeriya da ake kira Nollywood ke yi.
Fim din mai suna “The Black Book” ya shammaci duniyar fina-finai inda ya kasance cikin jerin fina-finai 10 fitattu a cikin harshen turanci a fadin duniya na tsawon makonni 3, sannan kuma ya zama na uku cikin mako na biyu.
Mutum miliyan 5.6 ne suka kalli tallar fim din cikin sa’o’i 48 bayan da aka sake shi a ranar 22 ga watan Satumba kana bayan mako biyu da ya fita, fim din ya kasance cikin jerin fitattun fina-finai 10 a kasashe 69 a cewar Netflix.
Masana’antar fina-finan Najeriya ta Nollywood ta zama abin misali tun daga shekarun 1990’ inda fina-finai irinsu “Living in Bondage” da Anikulapo da aka sake a shekarar 2022 suka kai mataki na daya a jerin fitattun fina-finan dandalin Netflix.
Nollywood ita ce masana’antar shirya fina-finai ta biyu a duniya bayan Indiya idan aka yi la’akkari da yawan fina-finan da take shirya wa, wadanda sukan kai 2,000 a duk shekara.
Akalla dala miliyan daya aka kashe wajen shirya wannan fim na “The Black Book” tare da hadin gwiwar wat tawagar kwararru.
“Shi fim ana yi ne saboda masu kallo, kuma samun masu kallo da yawa shi ne zai ba da damar aikewa da sako ga jama’a.” Editi Effiong da ya shirya fim din na “The Black Book,” ya fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na AP.
“Lokaci ya yi da duniya ya kamata ta kawo hankalinta kan masana’antar shirya fina-finan Najeriya.” Effiong ya kara da cewa.
A cewar kakakin Netflix, yanzu dandalin ya fi mayar da hankalinsa kan fina-finan da aka shirya su daga labaran da aka kirkiro su daga tushe na cikin gida a yankin kasashen da ke yamma da Sahara a Afirka.
“Afirka na da hazikan mutane, kuma mun dukufa wajen ganin mun saka hannun jari a nahiyar don mu ba da labarin Afirka daban-daban. Wata sanarwa da Netflix ta fitar ta ce.