Hukumar Kwallon Kafa Ta Ghana (GFA) Ta Sabunta Wa'adin Shugabanta

GFA BOSS, Kurt Okraku

A wani zabe da aka gudanar a babban taron hukumar a yankin arewacin kasar, Okraku ya samu gagarumar nasara, inda mutane 117 suka ba shi amincewarsu, wasu mutane ba su amince ba kana mutum guda bai halarci taron zaben ba.

GFA BOSS Kurt Okraku

Tsohon dan jarida na fannin wasannin ya kasance dan takarar daya tilo, bayan da kwamitin zabe da na daukaka kara a hukumar suka dakatar da abokin karawarsa George Afriyie saboda rashin cancanta, bayan kwamitocin sun zurafafa nazari a kan karar da Afriyie ya daukaka.

GFA BOSS Kurt Okraku Won Elelction

Okraku, tsohon shugaban kungiyar kwallo ta Dream FC ya kama aiki ne a ranar 25 ga watan Oktoban 2019 a farkon wa’adinsa na shekaru hudu.

Duk da barazanar neman kotu ta dakatar da zaben, jami’an Hukumar ta GFA sun ci gaba da gudanar da zaben.