Majalisar Dattawa Ta Hana Sanatocin Farko Yin Takarar Kujeran Shugaban Majalisar Dattawa Da Na Mataimakinsa

Taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

Majalisar dattawa ta yi wa dokar ta na gudanarwa gyaran fuska, inda aka hana sanatocin farko yin takarar kujeran Shugaban Majalisar dattawa da na mataimakinsa.

Amma wani masanin harkokin siyasa ya ce wannan ba abu ne da zai dore ba.

Majalisar ta yi wa Sashi na 2 da karamin Sashi 1,2 da 3 gyara, kamar yadda Shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ya nema a wani kuduri da ya gabatar a zauren Majalisar .

Kudurin mai taken gyara ga Kundin tsarin mulki na Majalisar dattijai ya zo ne bisa umarnin Yan Majalisar 109 Wanda aka yi a shekara 2022. Sanata Mai Wakiltan Jihar Neja ta Gabas Mohammed Sani Musa ya yi Karin bayani Kan gyara dokar da suka yi.

SENATOR MOHAMMED SANI MUSA

Sani ya ce dukkanin Yan Majalisa ne suka amince da wannan gyara, domin ba zai yiwu a bar wanda bai san yadda ake gudanar da Majalisa ba ya zama Shugabanta ba. Sani ya ce Majalisar ba ta yi wannan gyara don musguna wa wani ba, kawai an yi ne domin tabbatar da cewa Majalisar za ta ci gaba da samun alkibla, ba tare da kauce wa dokokinta ba, tunda su ne masu yin dokoki, ya kamata a gansu suna bin tsari

To ko mene ne gaskiyar cewa Majalisa tana Shirin tsige shugabanta Godswill Akpabio? Sai Sani ya bada amsa cewa babu Wanda zai tsige Akpabio, wani laifi ya yi? Majalisa tana bayansa, saboda duk abubuwan da ya fada a baya babu karya a ciki. Sani ya ce ana biyan 'yan Majalisar Dattawan Naira miliyan biyu kowannensu a lokutan bukukuwan Sallah da na Kirsimeti, da kuma duk lokacin hutu saboda za su koma mazabun su kuma an san dole ne su gudanar da ofisoshinsu na mazabu.

Godswill Akpabio

Sani ya karyata batun cewa Majalisar dattawa tana shirin tsige shugabanta Godswill Akpabio, inda ya ce babu wani laifi da Akpabio ya yi, saboda haka Majalisa tana bayansa. Babu Wanda zai tsige shi

Amma ga Masanin Harkokin siyasa na Kasa da kasa kuma Malami a jami'ar Abuja, Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi tsokaci Kan wannan mataki yana cewa a cikin siyasa wannan abu ne wanda ba abin mamaki ba ne, domin a duk lokacin da ake tafiya a siyasa ana tanadi ne na hana abokan hammaiya su samu dama akan wanda yake kan mulki, ko wanda ya ke tafiyar da mulkin, saboda haka idan Akpabio da mutanensa sun yi wannan tanadi, za a iya cewa ba abin mamaki ba ne.

Amma kuma abin da za a ji tsoro shi ne a ko yaushe a Majalisun tarayya duka guda biyu, idan an yi zabe ana juyar da yan Majalisa kusan kashi 70 suna kasa dawowa, sababbi ne suke zuwa, wadannan sababbi idan suka zo suka ga cewa ana ta tanadi akan hana su samun mukaman tafiyar da Majalisa, shin za su iya ci gaba da yadda da hakan, ko kuma an bude masu hanya yanzu, sun ga cewa an zama daya za a yi yunkuri kuma a samu nasarar gyara wadannan dokoki, wanda idan suka hada kansu watakila ba zai yi masu wahalar canzawa ba, su bude komai su mayar da shi duk ran da mutum ya zo, indai ya zama dan majalisa zai iya yunkurin bukatar neman ko wani irin mukami da ya ke cikin shugabancin Majalisar, saura da me, sai mun ga yadda gaba za ta nuna.

Kundin tsarin mulkin Majalisar dattawa ya bayyana cewa zabar Shugabannin a Majalisar zai kasance daidai da matsayin sanatoci wadanda aka sake zabansu, suka dawo Majalisar.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawa Ta Hana Sanatocin Farko Yin Takarar Kujeran Shugaban Majalisar Dattawa Da Na Mataimakin Sa