Majalisar Dattawa ta kore rahoton da ke cewa wasu Sanatoci na shirin tsige Shugaban Majalisar Godswill Akpabio, a bisa wasu abubuwa da aka ce ya yi,.
Ce-ce-ku-cen ya biyo raba mukaman Kwamitoci da Akpabio ya yi da kuma yadda ake zarginsa da yin subul-da-baka a lokacin gudanar da Majalisar.
Koda yake, Majalisar ta karyata yunkurin amma masana harkokin siyasa na cewa zai iya faruwa idan 'yan majalisar suna da hujjoji masu karfi.
Wata sanarwa mai dauke da sa hanun shugaban kwamitin yada labarai da hulda da jama'a na Majalisar, Yemi Adaramodu na cewa, wani labari da yake yaduwa a wasu sassa na kafafen yada labarai da ke cewa wasu 'yan majalisar na kulle-kullen tsige Shugaba Godswill Akpabio daga kasar Saudi Arabiya ba gaskiya ba ne.
Adaramodu ya ce babu kanshin gaskiya a labarin kwata-kwata domin kan 'yan majalisar dattawan a hade ya ke, saboda haka tsige Akpabio ba abu ne da zai iya faruwa cikin sauki ba.
Ya kuma kara da cewa, Majalisar Dattawa ta 10 tana gudanar da ayyukanta na yin doka kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar mata, kuma tana yin su da kyau domin amfanin 'yan Najeriya.
Sai dai masanin harkokin siyasa da zamantakewar dan Adam Kuma Malami a Jami'ar Abuja, Dokta Abu Hamisu yana ganin tsige shugaban Majalisar Dattawa abu ne mai yiwuwa idan an samu hujjoji masu karfi a kansa.
Hamisu ya kuma zargi 'yan siyasan Najeriya da kin bi wa talakan kasa hakkinsa, yana mai cewa abin da za su samu shi ne yake gaban su.
Ya kara da cewa, kudi na taka muhimmiyar rawa a wannan yunkurin domin 'yan Majalisa suna neman mayar da kudadensu da suka kashe a lokacin zabe.
Amma ga mai nazari kan al'amuran yau da kullum Aminu Jumare, shawara ce ya kecda ita ga 'yan Majalisar Dattawan.
Jumare ya ce in har ana so a cimma nasara kan wani yunkuri na tsige shugaban Majalisa sai sun kawar da kai kan kwadayi da son abin duniya
Shi ma Malami a Jami'ar Abuja kuma Kwararre a Fanin Diflomasiyar Kasa da Kasa, Dokta Farouk Bibi Farouk yana ganin tsige Akpabio ba abin mamaki ba ne, amma kuma da mamaki, saboda yaushe ma aka fara majalisar ta 10.
Manazarta na ganin batun yunkurin tsige Akpabio ya dan dade domin tun a watan Yuni maganar ta taso.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna