A makon jiya shirin ya maida tabo halin da masu bukata ta musamman ke ciki a Burkina Faso da irin gudunmowar da suke bayarwa a harakokin ci gaban al’ummar wannan kasa.
A kashi na farko na tantaunawar wakilin sashen Hamza Adams da Usman Mohammed mai kere kere kayayakin fata a Ouagadougou an ji yadda ya koyi wannan sana’a dake matsayin madogarar rayuwa a gareshi .
Sanin kaskancin da ke tattare da bara ya sa Malan Usman ware lokaci domin jan hankulan nakasassun da mutuwar zuciya da rashin samun kulawa daga al’umma suka jefa cikin wannan haraka.
To kashi na biyu kuma na karshen wannan tantaunawa zai maida hankali kan yanayin mu’amula a tsakanin masu bukata ta musamman da yadda abin yake a tsakaninsu da al’umma da kuma mahukuntan Burkina Faso.
Saurari shirin:
Your browser doesn’t support HTML5